Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta bayyana cewa: Tun a shekara ta 2000 al’ummar Lebanon suka tabbatar da cewa su ne jagororin gaskiya a kan tafarkin nasara
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta fitar da wata sanarwa a jiya Lahadi, inda ta jaddada cewa: Daidaiton sojoji da al’umma da kuma ‘yan gwagwarmaya da suke kare kasar Lebanon daga ha’incin makiya ba wai kawai tawada ne a takarda ba, don haka sun daurawa kasashen duniya karkashin jagorancin kasashen da suke daukar nauyin yarjejeniyar da aka cimma alhakin take hakki da laifuffukan makiya yahudawan sahayoniyya tare da tilasta mata ficewa gaba daya daga yankin Lebanon.
Tun daga shekara ta 2000 har zuwa yau, lamarin ya ci gaba da maimaita kansa, domin al’ummar kasar suna tabbatar da cewa: Su ne jagororin gaskiya a kan tafarkin nasara, tare da jarumtakarsu ta sake dawo da fatattakar makiya, tare da tabbatar da cewa babu wani mamaya a cikin wannan kasa mai albarka, wadda aka shayar da kowace hatsi a cikinta da jinin shahidai.