Dubban al’ummar kasar Jordan ne suka halarci gagarumar zanga-zanga a yau Juma’a a babban birnin kasar Amman, baya ga wasu da dama daga cikin lardunan kasar, suna rera taken samun nasara ga al’ummar Gaza da kuma nuna goyon baya ga ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa.
An kaddamar da zanga-zangar ce karkashin taken “Ba za mu bar Gaza ita kadai ba” tare da jaddada aniyar al’ummar Jordan ta ci gaba da nuna goyon baya ga gwagwarmayar Falasdinawa da kuma fafatukar kare kasarsu daga hatsarin yahudawan Sahayoniyya da Amurka.
A fadar mulkin kasar Amman, an gudanar da wani gagarumin tattaki da taron gangami a gaban Masallacin Al-Husain bayan sallar Juma’a, inda dubban ‘yan kasar ta Jordan suka halarta, domin nuna goyon baya ga tsayin Dakar al’ummar Zirin Gaza da suke fuskantar kisan kiyashi daga sojojin gwamnatin mamaya ta yahudawan sahayoniyya tare da samun cikakken goyon bayan soja da na siyasa da kuma na tattalin arziki daga gwamnatin Amurka.
Masu zanga-zangar sun jaddada yin kira ga daukacin al’ummar kasar Jordan da su gabatar da tasu gudunmuwar wajen samar da agaji ga al’ummar Gaza domin kalubalantar masifar yunwa da mazauna Zirin Gaza ke fama da ita sakamakon killace yankin da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi.
Har ila yau masu zanga-zangar sun bukaci gwamnatin kasarsu da ta yanke duk wata alaka da gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila, da yin watsi da yarjejeniyar Wadi Araba, da kuma soke yarjejeniyar tsaro ta hadin gwiwa da Amurka, kasancewarta abokiyar kawance ce a kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar Gaza.