Al’ummar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango Sun Nuna Fushi Kan Tsoma Baki A Harkokin Kasarsu

Masu zanga-zanga a birnin Kinshasa fadar mulkin kasar Dimokaradiyyar Kongo sun kai hare-hare kan ofisoshin jakadancin kasashe da suka hada da Amurka da Faransa Masu

Masu zanga-zanga a birnin Kinshasa fadar mulkin kasar Dimokaradiyyar Kongo sun kai hare-hare kan ofisoshin jakadancin kasashe da suka hada da Amurka da Faransa

Masu zanga-zangar sun kai hare-hare a wasu ofisoshin jakadanci a birnin Kinshasa, fadar mulkin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, a lokacin da suke gudanar da zanga-zangar a makon da ya gabata, don nuna adawa da yadda ake ci gaba da ruruta wutar rikici a shiyar gabashin kasar.

Shafin sadarwa na yanar gizo na Russia Today ya bayyana cewa: Al’ummar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango da suke cikin fushi sun kai hare-hare kan ofisoshin jakadancin kasashen Rwanda da Faransa da Belgium da kuma Amurka, yayin da hayaki ke tashi daga ginin ofishin jakadancin Faransa.

Masu zanga-zangar sun kona tutar Amurka tare da zargin kasashen yammacin duniya da goyon bayan ‘yan tawayen da suka karbe iko da birnin Goma da ke gabashin kasar.

A halin da ake ciki dai, sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, a wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban kasar Dimokaradiyyar Kwango Felix Tshisekedi, ya yi Allah wadai da harin da mayakan ‘yan tawayen M23 suka kai a birnin Goma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments