Alhazan Iran Suna Cigaba Da Dawo Wa Gida Daga Kasar Saudiyya

Kamfanin Jirgin sama na “Homa” ya sanar da cewa, a jiya Asabar kadai ya yi sawu 5 wajen dauko Alhajan Iraniyawa daga Saudiyya. Mahajjatan da

Kamfanin Jirgin sama na “Homa” ya sanar da cewa, a jiya Asabar kadai ya yi sawu 5 wajen dauko Alhajan Iraniyawa daga Saudiyya. Mahajjatan da za a  dauko daga Saudiyyar  za a sauke su ne a filiyen jiragen sama da suke a Karman dake kudancin Iran, sai kuma garin Ahwaz dake Kudu masu yammacin kasar,sai kuma birnin Masshad dake gabashin kasar sannan filin saukar jiragen sama na Imam Khumain ( r.a) dake Tehran.

Adadin Iraniyawan da su ka yi aikin Haji bana, sun kai 90,000, ba tare da wata matsala ta azo a gani ba.

Jakadan Iran a Kasar Saudiyya ya yabawa hukumar alhazan Iran saboda yadda ta tsara aikin Hajin, haka nan kuma kasar Saudiyya wacce ta kyautata karbar mahajjata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments