Rahotanni sun nuna cewa Afirka ta Kudu ta ce babu abin da zai sauya dangane da rashin zuwan wakilan Amurka taron G20 da take karbar bakuncinsa, bayan da shugaba Donald Trump a karshen makon jiya ya sanar da matakinsa bisa zargin cewa ana take hakkin dan adam a kasar.
Sanarwar da shugaba Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ta ce, mataimakin shugaban kasa JD Vance, wanda ake sa ran zai halarci taron shugabannin kasashen G20 a Johannesburg tsakanin 22 zuwa 23 ga Nuwamba, an soke ta bisa dalilai masu karfi.
Trump ya ce, abin kunya ne kwarai da gaske cewa za a gudanar da taron G20 a Afirka ta Kudu, kasar da ta kasance tana cin zalin wasu daidaikun mutane, ta hanyar kwace musu filaye da gonaki.
Amma ma’aikatar harkokin wajen Afirka ta Kudu ta bayyana wannan mataki a matsayin abin takaici tare da ci gaba da yin watsi da ikirarin.