Adadin Mutanen Da Sukayi Shahada A Hare-haren Isra’ila A Gaza Ya Kai 42,500

Ma’aikatar lafiya a Gaza ta bayyana cewa adadin falasdinawan da sukayi shahada a hare-haren Isra’ila tun fara yakin Gaza ya kai 42,500. Wannan ya hada

Ma’aikatar lafiya a Gaza ta bayyana cewa adadin falasdinawan da sukayi shahada a hare-haren Isra’ila tun fara yakin Gaza ya kai 42,500.

Wannan ya hada da sama da mutane 400 ne suka rasa rayukansu tun bayan da Isra’ila ta soma wano farmaki a arewacin Falasdinu.

A baya baya nan kuma akalla Falasdinu 19 sukayi shahada a harin Isra’ila a Gaza.

Ma’aikatar ta ce mutane 99,637 sun samu raunuka sakamakon hare-haren da ke ci gaba.

“Dakarun Isra’ila sun kashe 19 sun kuma raunana mutum 91 cikin wani kisan kiyashi da suka yi wa wasu iyalai cikin awanni 24 da suka gabata,” cewar ma’aikatar.

“Wasu tarin mutane sun makale karkashin baraguzan gine-gine da kuma tituna, yayin da ma’aikatan ceto suka kas cim musu”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments