Hukumomin kasar Afganistan sun sanar da cewa: Adadin mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasar da ta afku a gabashin Afghanistan ya haura 800, yayin da sama da 1,500 suka jikkata, adadin da ake sa ran zai karu.
Da sanyin safiyar yau Litinin ne, kamfanin dillancin labarai na RTA ya ruwaito hukumomin lafiya na kasar na cewa, suna ci gaba da kokarin gano hakikanin adadin wadanda suka mutu, yayin da suke ci gaba da kokarin isa wasu yankunan da lamarin ya shafa.
Ma’aikatar lafiya ta kasar ta sanar da cewa, Girgizar kasar ta lalata kauyuka uku a gundumar Konar gaba daya, yayin da wasu kauyukan suka samu munanan barna.
Tawagar ceto na kokarin gano wadanda suka tsira da rayukansu a yankin da ke kusa da kan iyaka da Pakistan, inda gidajen laka suka ruguje gaba daya.