Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Yemen ta sanar da cewa mutane 33 su ka yi shahada da kuma jikkata sanadiyyar hare-haren da Saudiyya ta kai a wani gida guda daya a garin Sa’adah,mafi yawancinsu yara ne da mata.
Ita kuwa tashar talabijin din ‘almasirah’ ta bayar da labarin cewa; jiragen yakin Saudiyyar sun kai wani harin akan tankin ajiyar Ruwan sha dake gundumar Dhali a kudancin Yemen.
A gundumar Shadaa dake kan iyaka kuwa Saudiyyar ta yi amfani da manyan bindigogi ne wajen kai hare-hare.
Gabanin haka janar Yahya Sari mai Magana da yawun sojojin kasar ta Yemen ya sanar da cewa; jiragen yakin Saudiyya sun kai hare-hare har sau 110 da kuma harba makamai masu linzami a cikin sa’o’i 24.
Jumillar hare-haren na Saudiyya daga fara yakin sun kai 2,652.