Adadin Falasdinawan Da Sukayi Shahada A Hare-haren Isra’ila Ya Kai 44,211

Ma’aikatar lafiya a Gaza ta sanar a ranar Lahadin nan cewa, adadin mutanen da sukayi shahada a hare-haren Isra’ila ya kai 44,211 tun bayan fara

Ma’aikatar lafiya a Gaza ta sanar a ranar Lahadin nan cewa, adadin mutanen da sukayi shahada a hare-haren Isra’ila ya kai 44,211 tun bayan fara yaki da Isra’ila fiye da shekara guda da ta wuce.

Akalla mutane 35 ne aka kashe a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, in ji sanarwar, inda ta kara da cewa mutane 104,567 ne suka jikkata a zirin Gaza tun soma yakin, bayan harin da Hamas ta kai wa Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba. 2023.

Isra’ila dai ta yi kunnen uwar shegu game da kiraye-kirayen da kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa ke ma ta na ta dakatar da kai hare-haren.

Amma a ranar Alhamis data gabata kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta fitar da umarnin kame firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan yakinsa Yoav Gallant bisa laifukan yaki da suka aikata a Gaza.

Batun dai ya fuskanci martani daga kasashen duniya dama.

Da yake kiran hukuncin da kotun ta ICC ta yanke, shugaban kasar Amurka Jo Baiden ya ce: “Bayar da sammacin kama shugabannin Isra’ila ya wuce gona da iri.

Tun da farko dama Amurka dake zaman babbar kawa ga Isra’ila ta ki amincewa da daftarin tsagaita wuta a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya domin dakatar da kisan kiyashin da Isra’ila ke yiwa al’ummar Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments