Adadin Falasdinawa Da Suka Yi Shahada A Gaza Sun Kai 44,000 Baya Ga Dubbai Da Suka Jikkata

Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da irin na yahudawan sahayoniyya a kan Gaza ya kai Falasdinawa 44,000 Ma’aikatar lafiya ta Gaza

Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da irin na yahudawan sahayoniyya a kan Gaza ya kai Falasdinawa 44,000

Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta fitar da rahoton kididdiga na yau da kullum kan Falasdinawa da yakin kisan kare dangi da yahudawan sahayoniyya suke ci gaba da yi kan Zirin Gaza a tsawon kwanaki 409, ya kai Falasdinawa 44,000.

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta ce: Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila’ sun aiwatar da kisan kiyashi har sau 4 kan iyalan Falasdinawa a Zirin Gaza da suka kunshi shahidai 76 da jikkata wasu 158 da aka garzaya da su zuwa asibitoci.

Ma’aikatar lafiyar ta yi nuni da cewa: Har yanzu akwai adadin wadanda abin ya rutsa da su a karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna, kuma motocin daukar marasa lafiya da jami’an tsaron farin kaya ba za su iya isa gare su ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments