Search
Close this search box.

Abdulsalam: Taimakon Amurka Ga Isra’ila A Kisan Mutanen Gaza Ta’addanci Ne Na Gaske

Kakakin kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: Taimakon da Amurka ke baiwa Isra’ila kan aikata laifuka a Gaza nuni ne na ta’addanci na

Kakakin kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: Taimakon da Amurka ke baiwa Isra’ila kan aikata laifuka a Gaza nuni ne na ta’addanci na hakika, wanda ke zama babbar barazana ga zaman lafiyar duniya.

A rahoton al-Masirah, Muhammad Abd al-Salam shugaban kwamitin tattaunawa na kasa kuma kakakin kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, ya gargadi kasashen duniya masu ‘yanci kan hadarin da ke tattare da yaduwar rudani a duniya daga ayyukan  gwamnatin Amurka.

A cikin jawabin nasa, ya bayyana goyon bayan da Washington ke bai wa ‘yan mamaya a Gaza a matsayin misali na ta’addancin kasa tare da fayyace cewa: kisan gillar da gwamnatin sahyoniya ta yi da hadin gwiwar Amurka a zirin Gaza laifi ne na karni a ci gaba da aiwatar da munanan manufofi na Isra’ila a gabas ta tsakiya.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da ayyukan da ake yi a tekun Bahar Rum na tallafawa al’ummar Palastinu, kakakin kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya bayyana cewa: Matsayin kasar Yemen ta hanyar ayyukan sojan ruwa shi ne goyon bayan wadanda aka zalunta a Gaza, wadanda Amurka ad isra’ila da ‘yan korensu suke yi wa kisan kare dangi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments