Tashar Talabijin din “ Almanar” ta sanar da cewa, da marecen yau Lahadi ne babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim sai yi jawabi akan muhimman abubuwan da suke faruwa a Lebanon da kuma wannan yankin.
Har ila yau, Almanar ta ce babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim zai yi bayani akan lokacin da za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah.
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah ya yi shahada ne a sanadiyyar hare-haren masu muni da jiragen yakin HKI su ka kai wa unguwar Dhahiya dake birnin Beiruta. Majiyar ‘yan sahayoniya ta ce sun jefa bama-bamai da su ka nai nauyin tan 85 akan ginin da Shahid Sayyid Hassan Nasrallah yake ciki.