Dr. Ali Larijani wanda yana cikin masu bayar da shawara ga jagoran juyin juya halin musulunci, kuma memba a cikin majlisar fayyace maslahar tsarin musulunci, zai ziyarci Syria ne domin ya gana da shugaba Basshar Asad da kuma manyan jami’an gwamnatin kasar.
Sanarwar ta fito ne daga kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, “Isma’ila Baka’i” a jiya Laraba.
Bugu da kari sanarwar ta ce, Dr. Larijani zai jagoranci tawagar gwamnati, kuma tattaunawar tasu za ta mayar da hankali ne akan halin da ake ciki a wannan yankin da kuma alakar kasashen biyu.