A cigaba da kai hare-hare na wuce gona iri da HKI take yi, da safiyar yau sun kai hari da jiragen yaki akan yankin Gaza da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 11.
Jiragen yakin HKI sun kai harin ne akan wani rukunin gidaje dake sansanin ‘yan hijira na “ Alburaij’ da kuma Nusairat’ wadanda suke a tsakiyar yankin Gaza, da hakan ya yi sanadiyar shahadar mutane 11.
A wata sanarwa da ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinawa ta fitar ta sanar da cewa, ya zuwa yanzu adadin shahidan Falasdinawa sun kai 38,000 da 882.
An shiga watanni na 10 da fara kai wa yankin Gaza hare-hare da HKI take yi,wanda har yanzu tana cigaba da yin kisan kiyashi a sassan Gaza mabganbanta.
A gefe daya wani daga cikin jagororoin kungiyar gwgawarmaya ta “Hamas” “Izzat al-Rashaq” ya ce; Amurka tana bayar da cikakken goyon baya ga dukkanin laifukan da HKI take tafkawa a cikin zirin Gaza.