A Jiya Alhamis Ne Aka Yi Juyayin 40 Na Shahadar Shugaban Kasar Iran Tare Da  Masu Rufa Musu Baya

A jiya Alhamis din an yi taron juyayin cikar kwanaki 40 daga shahadar Shugaban kasar Iran Hujjayul-Islam Ra’isi a babban masallacin Tehran, da dubun dubatar

A jiya Alhamis din an yi taron juyayin cikar kwanaki 40 daga shahadar Shugaban kasar Iran Hujjayul-Islam Ra’isi a babban masallacin Tehran, da dubun dubatar mutane su ka sami halarta.

Mahalarta taron juyayin sun daga hotunan sugaban kasar Shahidi, tare da maganganun da jagoran juyin musulunci ya yi a kansa.

 Shugaban kasar Iran na 8 Sayyid Ibrahim Ra’isi tare da ministan harkokin wajensa, Hussain Amir Abdullahiyan sun yi shahada ne a ranar 19 ga watan Mayu sanadiyyar faduwar jirgin sama maras matuki da yake dauke da su a gundumar Azerbaijan, dake kan iyaka da jamhuriyar Azerbaijan. Wasu da su ka yi shahada da shi, sun hada da babban limamin Tabriz Ali Hashim da kuma gwamnan jihar ta Azarbaijan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments