A Gobe Ne Harin “ Guguwar Aqsa” Yake Cika Shekara Daya

A gobe, 7 ga watan Oktoba ne dai yakin da HKI ta shelanta akan al’ummar Falasdinu yake ciki shekara daya, ba tare da ta cimma

A gobe, 7 ga watan Oktoba ne dai yakin da HKI ta shelanta akan al’ummar Falasdinu yake ciki shekara daya, ba tare da ta cimma manufofin da ta shelanta ba.

Tun farkon da HKI ta fara kai wa Falasdinada a Gaza hare-hare ta sanar da cewa, za ta rusa kungiyar Hamas, da kwace makamanta sannan kuma da raba ta da tafiyar da yankin Gaza.

Sai dai har ya zuwa yau da kasa da sa’o,i 24 ne su ka rage yakin ya cika shekara daya, babu daya daga cikin wadannan manufofin da ‘yan sahayoniyar su ka cimmawa.

Har yanzu kungiyar Hamas da sauran kungiyoyin gwgawarmaya a Falasdinu, suna cigaba da kai hare-hare da yin kwanton bauna akan sojojin HKI tare da kashe su.

Idan akwai wata nasara da HKI ta samu ya zuwa yanzu, ba ta wuce ta kashe fararen hula ba, da mafi yawancinsu mata ne da kananan yara.  Bugu da kari, sojojin HKI sun kuma rusa gidajen fararen hula da kuma lalata duk wasu abubuwa masu amfani na alumma da su ka hada da asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya.

Har ila yau, HKI ta tafka wasu laifukan yaki da su ka hada da kashe ‘yan jarida, da kuma amfani da makaman da aka haramta amfani da su a duniya.

Fiye da Falasdinawa dubu arba’in da daya ne dai su ka yi shahada, yayin da wasu dubun dubata su ka jikkata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments