Guterres Ya Damu Matuka Game Da Farmakin Isra’ila A Yammacin Kogin Jordan

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce ya damu matuka dangane da hare-haren soji da Isra’ila ke kai wa yankin Yammacin Kogin Jordan

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce ya damu matuka dangane da hare-haren soji da Isra’ila ke kai wa yankin Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye, yana mai kira da a gaggauta kawo karshen lamarin a yankin Falasdinu.

A cikin wata sanarwa, Guterres ya yi kira ya yi kira ga Isra’ila ta gaggauta dakatar da ayyukan sojinta a Gabar yamma da kogin Jordan da ta mamaye.

Da sanyin safiyar Larabar data gabata ce, sojojin Isra’ila suka gudanar da wani gagarumin farmaki a yankin yammacin kogin Jordan, inda suka tura daruruwan sojoji tare da kai hare-hare ta sama kan Jenin, Tulkarem, da Tubas.

Akalla Falasdinawa 17 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai a garuruwan, tare da jikkata wasu da dama.

An kashe takwas daga cikinsu a Jenin, biyar a Tulkarm, hudu kuma a Tubas, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Wafa ya ruwaito, daga  majiyoyin lafiya.

Guterres ya yi Allah wadai da asarar rayuka da suka hada da kananan yara, ya kuma bukaci Tel Aviv da ta kare fararen hula tare da tabbatar da tsaron lafiyarsu.

“Duk wadanda suka jikkata dole ne su sami damar samun kulawar lafiya, kuma ma’aikatan jin kai dole ne su iya kaiwa ga duk wanda ke bukata,” in ji babban jami’in MDD.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments