Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya bayyana cewa a halin yanzu HKI bata da karfin kare mutanen kasarta, saboda makaman makiya suna isa har tsakiyar kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Kan’ani yana fadar haka a safiyar yau Litinin, ya kuma kara da cewa hare-haren da dakarun Hizbullah suka kai kan HKI wanda aka sanya masa suna “hare haren 40’ sun tabbatar da cewa hatta yahudawan da suke rayuwa a babban birnin kasar ba sa cikin amince daga makaman Hizbulla da kuma sauran kasashe masu gwagwarmaya a yankin.
A safiyar jiya Lahadi ce dakarun kungiyar Hizbulla suka cilla makamai masu linzami kimani 320 kan wurare daban daban a cikin kasar Falasdinu da aka mamaye, daga cikin har da wasu wurare a birnin Tel’aviv babban birnin haramtacciyar kasar.
Shugaban kungiyar Sayid Hassan Nasarallah ya tabbatar da cewa ‘hareharen 40’ sun sami nasara, don makaman kungiyar sun sami bararsu kamar yadda aka tsara.