Hamas ta caccaki Isra’ila kan ƙin amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Wani babban kusa a kungiyar Hamas ya soki firaministan Isra’ila a kan ƙin amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, yana mai cewa zaman dakarun

Wani babban kusa a kungiyar Hamas ya soki firaministan Isra’ila a kan ƙin amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, yana mai cewa zaman dakarun Isra’ila a kan iyakar Masar na cikin manyan kalubalen da ake fuskanta.

Tawagar Isra’ila ta je Alkahira “domin tattaunawa kan sako mutanen da aka yi garkuwa da su”, in ji Omer Dostri, mai magana da yawun Benjamin Netanyahu a hira da AFP.

Sai dai wakilan Hamas ba sa cikin tattaunawar kuma babban jami’in ƙungiyar, Osama Badran, ya shaida wa AFP cewa dagewar da Netanyahu ta ci gaba da kasancewar dakarunsu a yankin Philadelphi na an iyaka ta nuna “kin yarda a kammala yarjejeniyar tsagaita wuta”.

Isra’ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla huɗu, ciki har da wani yaro a hare-hare biyu ta sama da jiragen yaƙinta suka kai kan tarukan fararen-hula a kudancin Gaza da tsakar dare. Kazalika gomman mutane sun jikkata.

Likitoci a Asibitin Nasser sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Falasɗinu (WAFA) cewa an kai musu gawawwakin mutum uku, ciki har da wani yaro, bayan harin da Isra’ila ta kai a garin Abasan.

Bugu da ƙari, jiragen yaƙin Isra’ila sun kai hari a yankin Zaytoun a Birnin Gaza inda suka kashe mutum ɗaya tare da jikkata da dama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments