Iran Ta Kama Yayan Kungiyar Yan Ta’adda Ta Daesh 14 Suna Kokarin Aiwatar Da Ayyukan Ta’addanci A Cikin Kasar

Ma’aikatar leken asiri ta kasar Iran ta bada sanarwa kama yan ta’adda daga kungiyar Daesh a cikin kasar, suna kokarin aiwatar da wasu ayyukan ta’addanci

Ma’aikatar leken asiri ta kasar Iran ta bada sanarwa kama yan ta’adda daga kungiyar Daesh a cikin kasar, suna kokarin aiwatar da wasu ayyukan ta’addanci a cikin kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar leken asirin kasar na bada wannan rahoton a safiyar yau Jumma’a.

Ta kuma kara da cewa yan ta’addan y’ay’an kungiyar ‘Daesh Khurasan’ ne, masu samun goyon bayan HKI da Amurka.

Labarin ya kara da cewa an kama 7 daga cikinsu a lardin Fars na kudancin kasar, a yayin da sauran kuma an kama su a lardunan Tehran, Albos, da kuma Khuzustan. Ma’aikatar ta kara da cewa yan ta’addan sun shiga kasar Iran ne a cikin yan kwanakin da suka gabata ba kuma tare da samun Visa ba, don aiwatar da ayyukan ta’addanci.

Banda haka ta kara da cewa, bayan wasu ayyukan bincike daban daban wadanda ma’aikatar hukumar suka gabatar, sun sami nasarar kama yan ta’addan tun kafin su kai hare haren da suka tsara zasu aiwatar a wurare daban daban a cikin kasar. Daga karshen sanarwan tace akwai cikekken bayani dangane da su nan gaba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments