Iran Ta Kafa Wasu Sharudda Na Komawa Kan Teburin Tattaunawa Da Kasashen Yamma

Sabon ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi, bayan ya tsallaka tantancewar majalisar dokokin kasar, a tattaunawasa ta farko da kafafen yada labarai ya

Sabon ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi, bayan ya tsallaka tantancewar majalisar dokokin kasar, a tattaunawasa ta farko da kafafen yada labarai ya bayyana cewa, a mataki na farko wanda ma’aikatarsa za ta dauka don sake farfado da yarjeniyar JCPOA ta shirin Nukliyar kasar Iran, da kuma rage matsalolin tsakanin Iran da Amurka da kuma kasashen yamma, ma’aikatar ta samarda wasu sabbin sharudda don hakan.

Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto Araqchi yana fadar haka a yau Jumma’a, sannan ya ce, idan turawan suna son a sake farfodo da hulda tsakaninsu da Iran to dole ne su ajiye sharuddansu wadanda Iran ba zata taba amincewa da su ba, don tafiya a kan al-amura wadanda bangarorin biyu suka amince da su.

Yace Iran tana son ganin an dauke takunkuman zalunci wadanda kasashen yamma suka dorawa JMI, sannan a koma harkokin na kasuwanci da na siyasa da sauransu kamar yadda suke hulda da duk sauran kasashen duniya.

Har’ila yau a hirarsa da kamfanin dillancin labaran ‘Kiyudo’ na kasar Japan, Sayyid Araqchi ya bayyan cewa a jawabin da ya gabatar a gaban yan majalisar dokokin kasar, a lokacin da yake bayyana shirinsa a ma’aikatar harkokin wajen kasar, ya ce: manufar daukewa kasar takunkuman tattalin arziki, musamman wadanda suka kasance daga bangare guda, za ta samu ne kawai, ta hanyar tattaunawa da fahintar juna tsakanin Iran da wadannan kasashe. Sannan a cikin lokacin da aka ayyana. Tare da kuma kiyaye manufofin JMI gaba daya a cikin tattaunawar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments