Jirgin Leken Asiri Na Kungiyar Hizbullah Ya Yi Shawagi Kan Gidan Natanyahu

Jirgin saman daukar hotunan leken asiri na kungiyar Hizbullah wanda ake sarrafashi daga nesa, ya yi shawagi kan gidan firai ministan HKI Benyamin Natanyahu da

Jirgin saman daukar hotunan leken asiri na kungiyar Hizbullah wanda ake sarrafashi daga nesa, ya yi shawagi kan gidan firai ministan HKI Benyamin Natanyahu da ke tsakanin birnin Tel-Aviv da kuma Haifa na bakin ruwa, ba tare da kayakin aikin soje na HKI da kawayenta da suke yankin sun gano shi ba.

Kamfanin dillancin labaran IRIB-NEWS ya bayyana cewa a lokacinda sojojin yahudawan suka fahinci cewa akwai wani jirgin saman daukar hotuna na Hizbullah a yankin sun tada jiragen saman yaki guda biyu don nemansa da kuma kakkaboshi amma sun kasa yin haka.

Gidan Natanyahu dai yana wani wuri da ke kira Kaisariyya a bakin Tekun Medeterian, sai dai wata majiya ta bayyana cewa tun lokacinda Iran ta bada sanarwan zata dauki fanasar jinin kissan Isma’ila Haniyya, firai ministan da iyalansa suka kasa kwana a gidansa da ke Kaisariyya. Ko kuma ba wanda ya san inda suke kwana.

Masana a ciki da wajen HKI sun tabbatar da cewa nasarar da kungiyar ta samu na aika jirgin saman leken asiri zuwa Kaisariyya ya tabbatar da cewa, da HKI zata shiga yaki da Kungiyar, da kuwa zata ji kunya, kuma zata shiga wani mummunan hali, don ba zata iya yaki da kungiyar ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments