Wani Jami’in Diblomasiyyar Kasar Burtaniya Ya Ajiye Aikinsa Saboda Kissan Kiyashi A Gaza

Wani babban jami’in diblomasiyya a ma’aikatar harkokin wajen kasar Burtaniya ya yi murabus daga mukaminsa don nuna rashin amincewarsa da ci gaban da aikawa HKI

Wani babban jami’in diblomasiyya a ma’aikatar harkokin wajen kasar Burtaniya ya yi murabus daga mukaminsa don nuna rashin amincewarsa da ci gaban da aikawa HKI makamai wanda gwamnatin kasar Burtaniya take yi.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa Mark Smith jami’a mai kula da ayyukan yaki da ta’addanci a ofishin jakadancin kasar Burtaniya da ke birnin Dublin na kasar Island ya bayyana cewa, da shi da abokan aikinsa, suna ganin yadda sojojin HKI suke kisan fararen hula suna satar kayakinsu a Gaza, wanda hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa, kuma don haka shi ba zai iya ci gaba da aiki a cikin wannan halin ba.

Smith, a cikin wasikar barin aikin da ya rubuta, wanda kuma ya aikawa abokansa kofinta, ya ce:  Jami’an gwamnatin HKI a fili ko wa na gani sun bayyana anniyarsu ta shafe al-ummar Falasdinu a Gaza da kuma Falasdinu gaba daya.

Ya ce: sojojin HKI banda kisa da kuma korar falasdinawa daga gidajensu, sun rusa kashi 80% na gine-ginen Gaza, sun kuma bata hatta yanyoyin da motuci suke bi a yankin. Suna hana kayakin agaji shiga Gaza, suna hana jami’an agaji isa inda falasdinawa mabukata suke, don taimaka masu. Wannan ya sa Falasdinawa da dama suka rasa rayukansu  saboda rashin samun taimako.

Daga karshe Smith ya ce, duk wadannan ko wannensu laifin yaki ne a bisa dokokin kasa da kasa.

Kafin haka dai ma’aikatar kiwaon lafiya a Gaza ta tabbatar da cewa an kashe fiye da mutane 40,000 a gaza a yayinda wasu fiye dubu 92 suka ji rauni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments