Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Amurka Da Birtaniya Sun Dade Suna Juyin Mulki A Kasashe

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Babban abin kunyar juyin mulkin shekara ta 1953 a Iran ba za ta gushe a goshin Amurka

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Babban abin kunyar juyin mulkin shekara ta 1953 a Iran ba za ta gushe a goshin Amurka da Burtaniya ba

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya bayyana cewa: Babban abin kunyar da aka yi sakamakon hambarar da zababben fira ministan kasar Iran Mohammed Mosaddiq a ranar 19 ga watan Agustan shekara ta 1953, tare da goyon bayan sojoji da jami’an tsaro da kuma siyasar mulkin kama karya da danniya, za su dawwama a goshin gwamnatocin Amurka da Birtaniya.

Dangane da tunawa da ranar 19 ga watan Agustan shekara ta 1953, Nasir Kan’ani ya rubuta a shafinsa na sada zumunta na yanar gizo cewa: Bautarwa, mulkin mallaka, juyin mulki da kuma tsoma bakin soja a harkokin wasu kasashe, ba wani abu ba ne sai dai wani bangare ne na tarihin ayyukan zalunci da nuna fin karfi da kasashen Amurka da Birtaniya suka shahara da su tsawon lokaci a wannan duniya.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya kara da cewa: Abin kunyar da Amurka da Birtaniya suka aikata na hambarar da zababben fira ministan Iran Mohammed Mosaddiq a ranar 19 ga watan Agustan shekara ta 1953, da kuma goyon bayan sojoji da jami’an tsaro da kuma siyasar zalunci da babakere munanan al’amura ne da za su ci gaba da wanzuwa har abada a gaban goshin gwamnatocin Amurka da Birtaniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments