Dakarun Kai Daukin Gaggawa Sun Kashe Mutane 80 A Jihar Sennar Ta Kasar Sudan

Mutane 80 ne suka mutu a wani hari da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kai a jihar Sennar da ke kasar

Mutane 80 ne suka mutu a wani hari da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kai a jihar Sennar da ke kasar Sudan

Akalla mutane 80 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon hare-haren da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kaddamar kan kauyen Galingi da ke jihar Sennar a kudu maso gabashin Sudan, kamar yadda majiyoyin lafiya da shaidun gani da ido suka ruwaito.

Wata majiyar lafiya ta bayyana cewa: Jami’anta sun isa asibiti inda suka tarad da gawawwakin mutane 55, wasu da dama kuma suka samu raunuka, ciki har da wadanda suke cikin mawuyacin hali, inda a sanyi safiyar washe gari mutane 25 daga cikinsu suka, wanda adadin ya kai 80. Wani mazaunin kauyen ya ce a lokacin da yake raka dansa da ya samu rauni zuwa asibiti, ya ga wasu motoci uku dauke da mayaka da makamai sun zo suka tunkari jama’a a gidajensu da suke kauyen, don haka mutane suka fito suka yi taho-mu-gama da su.

Bayan arangama maharan sun janye amma baya wani dan gajeren lokaci sun dawo da karfi da motoci sama da goma, kuma sun yi harbin kan mai uwa da wabi, lamarin da ya yi sanadin mutuwa mutane. Kamar yadda wata majiya ta rawaito cewa: ‘Yan bindigar sun kona gidajen jama’a, yayin da wasu gawarwakin jama’a suka zauna na tsawon sa’o’i a sararin samaniyya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments