Kasar Cuba Ta Bukaci A Gurfanar Da HKI Kan Laifukan Yaki Da Take Aikatawa A Gaza

Gwamnatin kasar Cuba ta bukaci a gurfanar da HKI kan laifukan yakin da ta aikata a Gaza. Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya

Gwamnatin kasar Cuba ta bukaci a gurfanar da HKI kan laifukan yakin da ta aikata a Gaza.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Cuba, Bruno Rodriguez yana fadar haka ya kuma bukaci a kawo karshen rigar kariyar gurfana a gaban kuliya wanda ake bawa HKI dangane da kissan kare dangin da take aikatawa a Gaza tun ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata.

Ya zuwa yanzu dai an kashe Falasdinawa fiye da 40,000 a yayinda wasu kimani 92,000 suka ji rauni. Mafi yawan wadanda aka kashin mata da yara ne. Minmistan harkokin wajen kasar Cuba ya yi allawadai da kissan mutane fiye da 40,000 a gaza ya kuma bukaci kasashen duniya su taru su tilastawa HKI dakatar da kissan kiyashin na Gaza.

Kafin haka dai kotun kasa da kasa ta fidda sammacin kama shugaban gwamnatin HKI Benyamin Natanyahu da kuma wasu manya manyan jami’an gwamnatinsa. Haka ma ta fidda wata doka wacce ta bukaci HKI ta dakatar da yaki a Gaza, don ci gaba da hakan laifin yaki ne. Amma gwamnatin Natanyahu ta take dukkan wadan nan dokoki ta kuma ci gaba da kissan kiyashi a gaza, saboda tana samun goyon bayan Amurka da kasashen yamma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments