Bagheri : Amurka Ba Ta Cancanci Zama Mai Shiga Tsakani Ba

Jamhuriyar Musulunci ta Iran na da hakkin mayar da martani ga kisan shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Ismael Haniyeh. Da yake tsokaci game da

Jamhuriyar Musulunci ta Iran na da hakkin mayar da martani ga kisan shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Ismael Haniyeh.

Da yake tsokaci game da kisan gillar da Isra’ila ta yi wa shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas a birnin Tehran, babban jami’in diflomasiyyar riko na kasar Iran ya ce Jamhuriyar Musulunci tana da hakki na mayar da martani kan wannan laifi.

Sannan “Ta hanyar nuna goyon baya a fili ga zaluncin da sahyoniyawan suka aikata, Amurka ta dauki bangaranci da rashin iya taka rawa wanda a hakan bata tantanci zama a matsayin mai shiga tsakani ba.

Ministan harkokin wajen kasar ta Iran, Ali Bagheri Kani, ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Masar Badr Abdelatty da yammacin jiya Asabar.

Ya jaddada cewa gwamnatin Isra’ila tana aikata ta’asa a Gaza yayin da take nuna munafunci da yaudara a tattaunawar da ake yi da nufin tabbatar da tsagaita wuta a yankin da aka yi wa kawanya.

Ana dai ci gaba da matsa kaimi don tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, yayin da sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ke shirin kai ziyara yankin.

Shugaban Amurka, Joe Biden ya ce ana dab da cimma yarjejeniyar tsagaita wutar bayan shafe kwana biyu ana tattaunawa a birnin Doha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments