Iran: Shugaba Pezeshkiyan Ya Gabatarwa Majalisar Dokokin kasar Iran Sunayen Ministocinsa A Yau Lahadi

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya gabatar da sunayen majalisar ministocinsa kasa da makonni biyu da rantsar da shi a matsayin shugaban kasar. Tashar talabijin

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya gabatar da sunayen majalisar ministocinsa kasa da makonni biyu da rantsar da shi a matsayin shugaban kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa shugaban Pezeskiyan ya rubutawa shugaban majalisar dokokin kasar  Mohammad Bakir Kolibof wasika inda a ciki ya ambaci sunayen wadanda yake son su kasance cikin majalisar ministocinsa.

Bayan karban wasikar shugaban majaliasar ya bada sanarwan cewa majalisar za ta fara tattaunawa dangane da ministocin a zamanta na yammacin yau Lahadi sannan zata tsara yadda ministocin na sa zasu zo majalisar tare da rakiyar mutane 2 don gabatar da shirye shiryensu a ma’aikatunsu a gaban majaliasar.

Daga cikin fitattun fuskoki a cikin majalisar ministocin Pezeskiyan dai akwai wanda yake son nada shi ministan harkokin wake wato Abbass Araqchi wanda ya fara aiki a ma’aikatar harkokin wajen kasar a shekara 1989, sannan ya yi aiki a matsayin mataimakin jakadan Iran a kungiyar kasashen Musulmi ta OIC a birnin Jidda na kasar Saudiya. Sannan ya taba rike jakadan Iran a kasashen Finland da kuma Japan. Har’ila Araqchi ya zama shugaban tawagar tattaunawa dangane da shirin makamashin nukliya na kasar Iran wanda ake kita P5+1.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments