Jakadan kasar Iran a MDD ya musanta zargin cewa kasarsa tana son aiwatar da kashe-kashen jami’an siyasa a cikin kasar Amurka.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar sharia a kasar Amurka tana bada sanarwa, a ranar 6 ga watan Augusta da muke ciki kan cewa ta kama wani mutum mai suna Asif Merchant dan kasar Pakistan kuma dan shekara 46 a duniya, wanda yayi kokarin kashe wasu jami’an siyasa a kasar Amurka ba tare da samun nasara ba. Kuma mutumin yana da dangantaka da kasar Iran.
Kafafen yada labaran Amurka sun nakalto ma’aikatar shariar na cewa jami’an hukumar FBI sun bayanna cewa Asif yana shirin kashe wasu yan siyasar Amurka daga cikin har da tsohon shugaban kasar Donal Trump saboda umurnin da ya bayar na kissan Janar Shahid Kasim Sulaimani shugaban Rundunar Qudus na dakarun IRGC, da yayi a cikin watan Jenerun shekara ta 2020.
Iran ta zabi hanyar gurfanar da Trump a gaban koliya saboda umurnin kisan Janar Sulaimani da yayi, kuma JMI tana daukansa a matsayin mai laifi, da shi da duk wadanda suke da hannu wajen kissan shahid Sulaimani. Amma wannan bai sa ta yi hayar wasu mutane don kashe su a cikin kasar Amurka ba, inji ofishijin jakadancin Iran dake birnin NewYork.
Janar Qasim Sulaimani dai shi ne shugaban rundunar Qudus a cikin dakarun kare juyin juya halin musulunci a Iran ko IRGC, sannan shi ne ya jagorancin yaki da kuma kawo karshen kungiyar yan ta’adda ta Daesh ko ISIS a kasashen Iraki da Siriya tsakanin shekara ta 2014-2017.
Kamar yadda kowa ya sani, wasu jami’an gwamnatin Amurka sun tabbatar da cewa, Amurka ce ta kafa kungiyar Daesh saboda cimma manufofinta a kasashen Asiya ta yamma.