Dakarun kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sun bada sanarwan kai hare hare tare da amfani da jiragen yaki na kunan bakin wake kan sansanin sojojin HKI mai lamba 91 a garin iliit na arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto bayanin da kungiyar ta fitar a jiya Lahadi na cewa sun kai hare haren ne don tallafawa falasdinawa wadanda suke fafatawa da HKI a Gaza, da kuma saboda hare haren da sojojin HKI suka kai a kan wasu garuruwa a kudancin kasar Lebanon, wadanda suka hada da garin Al-Bazuriyya, Dair Saryan, da kuma Haulah.
Bayanin ya kara da cewa makaman sun fada kan sansanin sojojin HKI na 91 da ke Iliit sun kuma halaka sojojin yahudawan da dama wasu kuma sun jikata.
Jaridar Al-Ahad ta kasar Lebanon ta kara da cewa, bayan faduwar makaman a kan Iliit, ya kuma lalata sansanin, gobara ta tashi a yankin wanda girmansa ya sa ana iya hangensa daga nesa.