Pezeshkiyan: Kissan Haniyya A Teran Wani Kuskure Ne Babba Wanda HKI Ta Aikata

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiya ya bayyana cewa HKI ta aikata babban kuskure a lokacinda ta kashe shugaban kungiyar Hamas Isma’ila Haniyya a Tehran, kuma

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiya ya bayyana cewa HKI ta aikata babban kuskure a lokacinda ta kashe shugaban kungiyar Hamas Isma’ila Haniyya a Tehran, kuma ya yi kira ga dukkan kasashen musulmi su yi All…wadai da kissan da kuma abinda HKI take aikatawa a kasar Falasdinu da ta mamaye, musamman a Gaza.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bukaci dukkan kasashe da mutanen masu yenci a duniya su yi allawadai da kissan da HKI ta yiwa shugaban Hamas a Tehran. Sannan ya kara da cewa Iran ba zata taba kyalewa al-amarin ya wuce ba tare da ta dauki fansar jininsa ba.

Labarin ya kara da cewa shugaban ya bayyana haka ne a lokacinda yake ganawa da ministan harkokin wajen kasar Jordan Ayman Al-Safadi a jiya Lahadi. Ministan harkokin wajen kasar ta Jordan  ya mikawa shugaban sakon Sarkin Jordan Abdullahi na II, inda a ciki sarkin yake taya shi murnan zabensa a matsayin shugaban kasar Iran  ya kuma yi masa fatan Alkhairi da hakan.

A maida martani shugaba Pezeskiyan ya godewa sarki da kuma gwamnatin kasar Jordan kan taya murna, ya kuma kara da cewa manufar gwamnatin kasar Iran musamman gwamnati ta 14, ita ce fadada dangantaka da kasashen yankin musamman kasashen musulmi. Da kuma neman hadin kan kasashen musulmi saboda kawo karshen kissan kiyashin da HKI take aikatawa a Gaza.

Shugaban ya kammala da cewa kissan da HKI ta yiwa Isma’il Haniyya shugaban kungiyar Hamas a Tehran  ba karamin kuskure  ba ne, kuma Iran ba zata kyale ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments