Karin Mutane 93 Sun Mutu A Mummunar Zanga-zangar Bangladesh

Akalla mutane 93 ne suka mutu, ciki har da jami’an ‘yan sanda 14, da kuma wasu fiye da dubu daya da suka jikkata, a wani

Akalla mutane 93 ne suka mutu, ciki har da jami’an ‘yan sanda 14, da kuma wasu fiye da dubu daya da suka jikkata, a wani kazamin rikici tsakanin masu zanga-zangar kin jinin gwamnati da ‘yan sanda a Bangladesh, a daya daga cikin kwanaki mafi muni tun bayan fara zanga-zangar kimanin makonni uku da suka gabata.

Adadin wadanda suka mutu sakamakon zanga-zangar da akeyi a Bangladesh ya kai a kalla mutane 300 a ranar Litinin, bayan da aka kashe mutane 94 a ranar da ta wuce, yayin arangamar da aka yi tsakanin masu zanga-zangar da masu goyon bayan gwamnati, a cewar wata kidayar kamfanin dillancin labarai na AFP.

Alkalumman sun shafiu bayanai daga ‘yan sanda, jami’ai da likitoci a asibitoci.

A ranar Lahadi ‘yan sanda sun yi amfani da karfi don tarwatsa dubun dubatar masu zanga-zangar neman firaministan kasar Sheikh Hasina ta yi murabus.

Zanga-zangar da aka fara a watan jiya ta rikide zuwa tarzoma mafi muni a shekaru 15 na mulkin Hasina.

MDD, ta bayyana matukar damuwa game da halin da ake ciki a Bangaladesh.

“Dole ne a daina tashin hankali mai ban tsoro,” in ji babban jami’in kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya Volker Turk a cikin wata sanarwa.

Ya bayyana damuwar sa game da karin mace-macen da ake yi gabanin tattakin jama’a a Dhaka da aka shirya yi ranar Litinin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments