Gaza: Sojojin HKI Sun Aikata Wani Sabon Kissan Kare Dangi A Asbitin “shuhada-Alaksa’ A Safiyar Yau Lahadi

Sojojin HKI sun kai hare hare kan sansanin yan gudun hijira na Falasdinawa da ke cikin harabar asabitin shuhada- Al-Aksa dake tsakiyar zirin Gaza a

Sojojin HKI sun kai hare hare kan sansanin yan gudun hijira na Falasdinawa da ke cikin harabar asabitin shuhada- Al-Aksa dake tsakiyar zirin Gaza a safiyar yau Lahadi 4-8-2024.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto dan rahotonta a yankin yana cewa, yau ce ake cika kwanaki 303 da fara yakin tufanul Aksa kuma a dai dai wannan lokacin ne jiragen yakin HKI suka yi ruwan makamai masu linzami ta sama, a kan hemomin falasdinawa a asbitin, suka kuma yi sanadiyyar shahadar akalla Falasdinawa 5, a yayinda  wasu akalla 18 suka ji Rauni.

Wata majiyar Falasdinawa a yankin ta tabbatar da cewa za’a sami wasu Karin wadanda zasu yi shahada saboda asbitin ba zai iya kula da wasu wadanda suka ji rauni ba saboda basu da kayan aiki.

A jiya Asabar ma sojojin yahudawan sun aikata irin wannan kissan kiyashin a makarantar Hamamah da ke unguwar sheik Ridwan da ke arewacin zirin gaza inda a nan ma falasdinawa 15 suka yi shahada.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments