Mai kula ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya cewa: Dole ne al’ummun duniya su tashi tsaye wajen tunkarar haramtacciyar kasar Isra’ila
A tattaunawarsa ta hanyar wayar tarho da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a jiya Alhamis, mai kula da ma’aikatar harkokin wajen Iran Ali Baqiri Kani bangarorin biyu sun yi musayar yawu kan batun ayyukan ta’addancin da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa musamman na baya-bayan nan na kashe shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Isma’il Haniyyah a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Baqiri Kani ya jaddada cewa: Wannan ta’addancin da yahudawan sahayoniyya suka aikata wajen janyo shahadar Isma’il Haniyah a birnin Tehran, baya ga kasancewarsa keta hurumin Jamhuriyar Musulunci ta Iran kuma keta hurumin dokokin kasa da kasa ne da ke jefa zaman lafiya da amincin yankin da ma duniya baki daya cikin hatsari, yana mai jaddada cewa: Iran ba za ta yi watsi da hakkinta na kare kai da kuma daukar matakin hukunta yahudawan sahayoniyya masu laifi ba.
Haka nan Baqiri Kani ya yi nuni da bukatar Iran na gudanar da wani zaman taro na musamman na kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya kan yin Allah wadai da yunkurin Amurka da kasashen Turai na hana yin Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa Isma’il Haniyya a birnin Tehran, yana mai jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya suna yin barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya don haka dole ne al’ummar duniya su tashi tsaye wajen ganin sun taka burki ga wannan gungun ‘yan ta’adda masu aikata laifuka domin samun damar wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.