Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyid Abdul-Malik Badruddeen al-Houthi, ya tabbatar da cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya ta hanyar kara laifukan da suke yi, lamari ne da ke kara kusantar da su ga halaka da gushewa daga kan doron kasa da babu makawa, yana mai jaddada cewa; Shahadar shugabannin gwagwarmaya tana da matukar tasiri wajen karfafawa da kwadaitar da sauran mutane zuwa ga ci gaba da tafiya a kan hanyar gwagwarmaya, yayin da tafarkin jihadi ke karuwa kuma ake samun nasarori.
A jawabin da ya gabatar kai tsaye ga al’ummar Yemen kan ci gaban yakin Ambaliyar Al-Aqsa, Sayyid Abdul-Malik Badruddeen Al-Houthi ya jaddada cewa: Shahidi Isma’il Haniyyah shugaban ofishin siyasar kungiyar Hamas ya ba da gagarumar gudumawa wajen karfafa yin hidima ga gaskiya da adalci da kuma ‘yantar da al’ummar Falasdinu da Masallacin Al-Aqsa mai albarka.
Sayyid Houthi ya kara da cewa; Ko wane irin laifi haramtacciyar kasar Isra’ila da kawayenta Amurka da wasu kasashen yammacin Turai suke aikatawa, hakan ba zai raunana azamar Mujahidai da al’ummun da suke gwagwarmayar neman ‘yanci ba.