JMI Ta Bukaci Taron Gaggawa Na Kungiyar Kasashen Musulmi Bayan Kissan Shugaban Hamas Isma’ila Haniyya

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bakiri Kani ya bukaci taron gaggawa na kungiyar kasashen musulmi ta OIC don tattauna dangane da kissan shugaban

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bakiri Kani ya bukaci taron gaggawa na kungiyar kasashen musulmi ta OIC don tattauna dangane da kissan shugaban kungiyar Hamas Isma’ila Haniyya a nan birnin Tehran.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana  cewa, za’a gudanar da taron gaggawa na kasashen musulmi ne, bayan ya tattaunawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Saudiya Yerima Faisal Bin Farhan Ali Saud da Sheikh Muhammad bin Abdurrahman bin Jasim Althani da Badr Abdullatti ministan harkokin wajen kasar Masar da kuma Hakan Fidan ministan harkokin waje kasar Turkiyya.

Bakiri ya kara da cewa kafin hakan dukkan ministocin sun yi allawadai da kissan Isma’il Haniyya a Tehran, sun kuma dorawa HKI laifin kissan.

Bakiri Kani ya kara da cewa akwai bukatar taron kasashen musulmi da gaggawa don tattaunawa wannan batun.

Haniyya dai ya kasance fitaccen shugaba, wanda ya kasance abun girmamawa a cikin al-ummar Musulmi, saboda gwagwarmayan da yake jagoranta na samarwa Falasdinawa yencin kansu daga hannun yahudawan Sahyoniyya da masu goya masu baya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments