Kwamitin Tsaro Na MDD Ta Yi Allawadai Da Kissan Shugaban Kungiyar Hamas Isma’ila Haniyya A Tehran

Kwamitin tsaro na MDD ya yi allawadai da kissan da aka yiwa shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas Isma’ila Haniya a birnin Tehran. Kamfanin dillancin

Kwamitin tsaro na MDD ya yi allawadai da kissan da aka yiwa shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas Isma’ila Haniya a birnin Tehran.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa jakadan JMI a MDD Sa’eed Iravani ne ya bukaci taron gaggawa na kwamitin bayan ya sami labarin kissan Isma’ila Haniyya shugaban kungiyar Hamas a Tehran.

Shahid Haniyya dai ya zo Tehran ne don halattar bikin rantsar da sabon shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan wanda aka gudanar a ranar Talatan da ta gabata.

A taron kwamitin na jiya Laraba,  jakadan kasar China a MDD  Fu Cong, ya ce kasarsa tana all..wadai da wannan kissan kuma wannan babban zagon kasa ne ga zaman lafiya da ake bukata a gaza. Kuma kasar China ta damu da abinda zai biyo bayan wannan kissan.

Jakadan kasar Aljeriya a MDD Ammar bin Jaami’u, ya bayyana cewa, wata musiba babban tana gabammu. Ya kuma kara da cewa, kissan Haniyya babban kuskure ne kuma aikin ta’addancin ne. banda haka ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Kasar Rasha da wasu daga cikin kasashen a kwamitin, duk sun yi allawadai da kissan shugaban kungiyar ta Hamas a Tehran. Sun kuma bayyana damuwarsu da abinda zai biyu bayan hakan.

Jagoran juyin juya halin Musulunci a nan Iran, Imam Ayatullah Sayyid Aliyul Khaminae ya ce: wajibin JMI ne ta maida martani mai tsanani kan kissan Haniyya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments