Jakadan Kasar Siriya A Majalisar Dinkin Ya Yi Gargadi Yadda H.K.Isra’ila Take Cin Karenta Ba Babbaka

Wakilin kasar Siriya a Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi kan yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da yin watsi da dokokin kasa

Wakilin kasar Siriya a Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi kan yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da yin watsi da dokokin kasa da kasa

Wakilin kasar Siriya a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa: Kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suka yi wa shugaban ofishin siyasa kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas shahidi Isma’il Haniyeh, ya bayyana tunanin gwamnatin yahudawan sahayoniyya da ke wakiltar martaninta kan shiri da ake kira “Shirin Biden” wanda kudurin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2735 ya amince da shi.

Siriya ta yi gargadin cewa: Yadda ‘yan mamaya ke ci gaba da yin watsi da dokokin kasa da kasa da rashin yin aiki da kudurorin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da kiraye-kirayen da kasashe mambobin Majalisar ke yi na dakatar da kai hare-haren wuce gona da iri da kisan kiyashin da take yi, hakan ya sanya ta kunna wutan yaki a yankin baki daya tare da yin barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, tare da jaddada cewa: Wadannan hare-haren wuce gona da iri ba za su sa al’ummar yankin su yi watsi da zabin kasa ba, da kuma fafutukar da suke yi na ‘yantar da yankunan da aka mamaye musu ba bisa tawaye ga kudurori da dokokin kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments