Al’ummun Kasar Iran Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Yin Allah Wadai Da H.K.Isra’ila

Al’ummun garuruwa da lardunan kasar Iran sun fito zanga-zangar yi Allah wadai da harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai da ya yi sanadin shahadar

Al’ummun garuruwa da lardunan kasar Iran sun fito zanga-zangar yi Allah wadai da harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai da ya yi sanadin shahadar Isma’il Haniyah

Rahotonni sun watsa labaran cewa: An gudanar da gagarumar zanga-zanga a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran da wasu larduna da garuruwa da dama na yin Allah wadai da yin tir da wannan aikin ta’addanci na kai harin kan shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas na Falasdinu Isma’il Haniyyah da yahudawan sahayoniyya suka yi kan masaukinsa a birnin Tehran.

Masu zanga-zangar da suka taru a birnin Tehran sun yi Allah wadai da siyasar fuska biyu da masu rajin kare hakkin bil’adama a yammacin duniya suka dauka kan shahadar Isma’il Haniyyah tare da neman gwamnatin Iran ta hanzarta daukar fansa kan jinin shahidan.

A birnin Mashhad da ke arewa maso gabashin Iran, musamman a hubbaren Imam Ridha {a.s}, an shirya wata gagarumar zanga-zangar yin Allah wadai da Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila dangane da kisan gillar da ake yi wa Isma’il Haniyyah.

Kamar yadda a birnin Qum aka gudanar da taron yin Allah wadai da harin gilla gami da daga tutar wajabcin daukar fansa a saman kubbar Masallacin Jamkaran dake wannan birni mai alfarma.

Al’ummar birnin Ilam da ke yammacin kasar Iran, sun yi tir da ta’addancin haramtaciyar kasar Isra’ila na kai hari kan shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas. Haka nan Al’ummar lardin Sistan da Baluchestan sun yi Allah wadai da wannan harin ta’addancin da aka kai kan shahidi Ismail Haniyeh.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments