Kasashen Iran Da Gambiya Sun Dawo Da Alakar Diflomasiyya A Tsakaninsu

An samu kyautatuwar alaka da dawo da dangantakar diflomasiya tsakanin kasashen Iran da Gambiya A jiya litinin ne mai kula da ma’aikatar harkokin wajen kasar

An samu kyautatuwar alaka da dawo da dangantakar diflomasiya tsakanin kasashen Iran da Gambiya

A jiya litinin ne mai kula da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ali Baqiri ya karbi bakwancin ministan harkokin wajen kasar Gambiya, kuma a yayin ganawar jami’an biyu, mai kula da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran da ministan harkokin wajen kasar Gambiya, sun rattaba hannu kan wata sanarwa a hukumance dangane da maido da huldar jakadanci tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Jamhuriyar Gambiya.

Bayan zaman taron da manyan jami’an kasashen biyu suka gudanar a tsakaninsu a shekarun baya-bayan nan da kuma tattaunawar da aka yi a lokacin ziyarar, ministan harkokin wajen Gambiya Mamadou Tangara a birnin Tehran na Iran da kuma Ali Baqiri a gefen wurin bikin rantsar da sabon shugaban Iran Masoud Pezeshkian, bangarorin biyu sun yanke shawarar dawo da huldar jakadanci a ranar 29 ga wannan wata na Yuli na wannan shekata ta 2024 saboda kiyaye muradun kasashen biyu.

Gwamnatocin kasashen biyu sun amince da raya dangantakar abokantaka a tsakaninsu bisa tsarin mutunta juna, daidaito da kuma moriyar juna.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments