Wata kotu a nan Tehran ta saurari karar da aka shigar kan ayyukan ta’addancin Amurka a kasashen yammacin Asiya karo na biyu a yau Lahadi a nan Tehran.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa iyalan wadanda suka yi shahada a kasashen Siriya da Iraki suna daga cikin wadanda suka halarci zaman na yau Lahadi.
Wadanda suka yi Magana a gaban Alkali daga cikinsu sun bayyana cewa, kasar Amurka ta yi amfani da kungiyoyin yan ta’adda wadanda ta samar a yankin don yada ayyukan ta’addancin a kasashen Iraki da Siriya.
Kungiyoyin dai sun hada da Daesh, Annusra, Jaish Zulm da sauransu. Har’ila yau, Amurka ta yi amfani da wadannan yan ta’ada don kashe mutane da dama a wadannan kasashe biyu, har’ila yau ta yi amfani da su don kashe Iraniyawa wadanda suka yi shahada suna kokarin kare haramin Zainab (s) a kasar Siriya, da kuma haramomin limamai masu tsarki a kasar Iraki.
Alkalin da saurari karan a yau, shi ne Mai Sharia Hossienzadeh, ya kuma bayyana cewa ya zuwa yanzu, mutane 725 ne suka shigar da kararraki har 57 kan wadanda ake tuhuma 18 daga ciki har da gwamnatin Amurka.
Tun shekara ta 2011 ne kasashen siriya da Iraki suke fama da yan ta’adda wadanda Amurka da kawayenta na kasashen yankin suka kafa. A halin yanzu ma, wasu yan ta’addan suna ci gaba da iko da yankin Idlib na kasar Siriya. A yayinda ita Amurka take mamaye da rijiyoyin man kasarSiriya da ke kira Omari a arewacin kasar Siriya.