Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Iran Ali Bagheri Kani ya ce matakin “siyasa” da Jamus ta dauka na rufe Cibiyar Musulunci ta Hamburg (IZH) da rassanta da nufin biyan muradun gwamnatin Isra’ila.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock a ranar Asabar, Bagheri Kani ya yi kakkausar suka ga matakin wanda aka dauka ba bisa ka’ida ba, inda ‘yan sandan Jamus suka haramtawa wasu cibiyoyin Musulunci a kasar Turai, ciki har da cibiyar IZH gudanar da ayyukansu, tare da bayyana hakan da cewa ya saba wa ka’idojin kare hakkin bil’adama.
“Rufe cibiyoyin Musulunci a Jamus wani mataki ne na siyasa gaba daya da ya yi daidai da kyamar Musulunci da kuma biyan muradun gwamnatin Sahayoniya. in ji shi.
Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Jamus ta fada a ranar Laraba cewa “ta haramta Cibiyar Musulunci ta Hamburg da kungiyoyin da ke da alaka da ita a cikin Jamus, saboda abin da gwamnatin Jamus ta bayya da cewa cibiya ce mai tsattsauran ra’ayin Islama da ke bin manufofin da suka saba wa tsarin mulki.”
Ana zargin cibiyar da goyon bayan gwagwarmayar Hizbullah ta Lebanon, wadda Berlin ta ayyana a matsayin “kungiyar ‘yan ta’adda”, da kuma yada kyamar Yahudawa da ‘yan mulkin mallaka.
A wani bangare na dokar, ma’aikatar ta ce za ta kuma rufe masallatan ‘yan Shi’a guda hudu da suka hada da na Hamburg’s Blue Mosque, daya daga cikin tsofaffin masallatai a Jamus.
A nata bangaren, ministar harkokin wajen Jamus ta ce cibiyoyin Musulunci a Jamus za su iya bin kadun hakkokinsu ta hanyoyin da suka dace.
Baerbock ta jaddada mahimmancin warware bambance-bambancen tare da bayyana fatan cewa za a kawar da matsalolin da ake da su a dangantakar da ke tsakaninsu ta hanyar tattaunawa da diflomasiyya.