Hezbollah: ‘Isra’ila’ ce ke da hannu a harin Golan

Gwamnatin Biden ta bayyana damuwarta kan harin da aka kai jiya Asabar kan tuddan Golan na Syria da Isra’ila ta mamaye, wanda Amurka ke zargin

Gwamnatin Biden ta bayyana damuwarta kan harin da aka kai jiya Asabar kan tuddan Golan na Syria da Isra’ila ta mamaye, wanda Amurka ke zargin cewa “daga Labanon ne”, wanda a cewar Amurka zai iya kara tsananta yaki tsakanin Hizbullah da Isra’ila, a cewar rahoton Axios.

Zargin na Amurka dai na zuwa ne duk da cewa kungiyar ta Hizbullah ta musanta hakan, kamar yadda ta tabbatar wa Majalisar Dinkin Duniya cewa ba ta da hannu ko wata masaniya dangane da harin, Shafin Axios ya nakalto wani jami’in Amurka yana cewa jami’an Hizbullah sun shaidawa Majalisar Dinkin Duniya cewa lamarin da ya faru a Tuddan Golan ya faru ne sakamakon harin makami mai linzami da Isra’ila ta kai a filin wasan kwallon kafa.

Wani jami’in Amurka, da yake magana da Axios, ya nuna cewa wannan lamari na iya zama sanadin da gwamnatin ke fargaba da kokarin kaucewa tsawon watanni goma da suka gabata.

Nafiseh Kohnavard wata fitacciyar ‘yar jarida  ta yi karin haske a cikin wani sako da ta wallafa a shafin X cewa, tambayoyi da yawa sun dabaibaye abubuwan da suka faru a Majdal Shams.

Kohnavard ta ci gaba da cewa, harin da kungiyar Hizbullah ta kai cikin watanni goma da suka gabata ya shafi manufofin soji ne kawai. Ko bayan harin da aka kai kan kadarorin Isra’ila a matsugunan yahudawa, Hizbullah ta ba da hujjar cewa, ta dauki matakin hakan ne saboda sojojin Isra’ila ne ke amfani da wuraren a matsayin sansanoninsu na kai hari kan Lebanon.

Hizbullah ta musanta cewa tana hannu ko alhakin kai harin kauyen Majdal Shams da ke yankin tuddan Golan na Syria da Isra’ila ta mamaye, sabanin ikirarin Isra’ila kan lamarin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments