An Tsaurara Tsaro A Iyakokin Najeriya A Lokacin Da Ake Shirin Gudanar Da Zanga-Zanga

Gwamnatin Tarayya ta tsaurara matakan tsaro a dukkanin iyakokin Najeriya gabanin fara zanga-zangar da aka shirya yi a faɗin ƙasar a ranar 1 ga watan

Gwamnatin Tarayya ta tsaurara matakan tsaro a dukkanin iyakokin Najeriya gabanin fara zanga-zangar da aka shirya yi a faɗin ƙasar a ranar 1 ga watan Agusta.

Kwanturolan Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), Kemi Nandap ce, ta bayyana hakan a wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Kenneth Udo ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Nandap, ta umarci dukkanin shugabannin shiyya-shiyya a faɗin ƙasar da su yi taka-tsantsan a lokacin zanga-zangar.

Ta ce ya kamata jami’an hukumar su ƙara sanya ido kan zanga-zangar da wasu ƙungiyoyi ke shirin yi.

Ta kuma ce umarnin na da nufin tabbatar da cewa wasu ƙasashen waje ba su shigo cikin ƙasar domin shiga zanga-zangar ba.

“Dangane da alhakin kare iyakokin ƙasar da aka ɗora a wuyan hukumar, an ɗora wa jami’ai alhakin tabbatar da tsaron iyakokin ƙasar nan.

“Wannan shi ne ta hanyar tabbatar da cewa babu wani baƙon da zai iya fakewa da zanga-zangar don tada zaune tsaye a ƙasar nan,” in ji ta.

Hukumar ta dakatar da dukkanin hutun wucin gadi na jami’anta domin tabbatar da cewar komai ya tafi daidai a lokacin zanga-zangar.

Nandap, ta tabbatar wa daukacin ’yan Najeriya shirin hukumar na kiyaye iyakokin ƙasar domin inganta tsaro.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments