Rahotanni sun tabbatar da cewa, bayan da Isra’ila ta kwashe makonni tana kai musu hari babu inda za su je, ɗaruruwan Falasdinawa sun koma ɓuya a wani tsohon gidan yarin Gaza da aka gina domin tsare masu laifin kisan kai da ɓarayi.
Yasmeen al-Dardasi ta ce ita da ‘yan’uwanta suna ji suna gani suka dinga wuce wasu mutanen da suka samu raunuka da ba za su iya taimaka musu ba yayin da suke ƙaura daga wasu yankuna da ke kudancin birnin Khan Younis zuwa gidan yarin.
Sun yini a karkashin bishiya kafin su wuce zuwa tsohon gidan yarin, inda yanzu suke zaune a ɗan ƙaramin masallacin da ke wajen. Suna samun kariya daga zafin rana, amma babu sauran jin daɗi.
Mijin Dardasi yana fama da ciwon ƙodar da huhu, amma babu katifa ko bargo. “Mu ma ba mu zauna a nan ba,” in ji Dardasi, wadda kamar sauran Falasdinawan tana fargabar yaƙi ya sake cim mata.
A daya bangaren kuma Ɗaruruwan Falasɗinawa da Yahudawa na Isra’ila ne suka yi ta rera taken “E, a samu zaman lafiya, e, ga yarjejeniya”, a yayin wani tattaki da suka yi a birnin Tel Aviv, suna masu neman a kawo ƙarshen kashe-kashe da ake yi a Gaza.
Masu zanga-zangar sun ce ajandarsu ta farko ita ce a tsagaita wuta a yankin da aka mamaye, amma gaba ɗaya suna so a sake maido da dangantakar Falasɗinu da Isra’ila tare da ba da damar kafa sabuwar rayuwa.