Ma’aikatar lafiya ta Hamas a zirin Gaza ta sanar a yau Asabar cewa, wani harin da Isra’ila ta kai kan wata makaranta da ke tsakiyar yankin, ya yi sanadin shahadar mutane 30 tare da jikkata wasu fiye da 100.
“Makarantar Khadija, wacce ke dauke da rukunin likitocin wucin gadi a yankin Deir al-Balah, ta fuskanci hari daga sojojin Isra’ila in ji ma’aikatar.
A nasu bangare sojojin Isra’ila, sun yi nuni da cewa, sun kai wani samame a cikin makarantar inda suka kai hari kan mutanen da suka danganta da “yan ta’adda” da ke aiki a wurin.
Kafin hakan dama majiyoyin farar hula daga Gaza ta sanar a wannan Asabar, cewa, farmakin da Isra’ila ke ci gaba da kai wa tun ranar Litinin a Khan Younes ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 170 a ciki da wajen wannan gari mai yawan jama’a a kudancin zirin Gaza.
Daga bangaren Majalisar Dinkin Duniya kuma, ta bayyana, cewa daga ranar Litinin zuwa Laraba, sama da Falasdinawa dubu 182 aka tilastawa barin yankunan tsakiya da yammacin Khan Younis zuwa wasu sassa.
Yakin da Isra’ila ta kadddamar kan Falasdinu tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, ya yi sanadin mutane sama da 39,000 baya ga wau 11,000 wadanda ba a san makomarsu ba.