Birtaniya Ta Ce Ba Za Ta Yi Katsalanda Ga Bukatar Kotun (ICC) Na Neman A Kamo Netanyahu  

Gwamnatin Birtiniya ta sanar da cewa ba ta adawa da sammacin kame firaministan isra’ila Benjamin Netanyahu kamar yadda kotun Hukunta Manyan Laifuka ta kasa da

Gwamnatin Birtiniya ta sanar da cewa ba ta adawa da sammacin kame firaministan isra’ila Benjamin Netanyahu kamar yadda kotun Hukunta Manyan Laifuka ta kasa da kasa ta nema.

Ofishin Firaministan Burtaniya, Keir Starmer ya fada a ranar Juma’a cewa Burtaniya ba za ta yi katsalanda ga bukatar kotun ta (ICC) na neman a kamo firaministan Isra’ilar ba.

Wannan sanarwar ta ci karo da tsare-tsaren da tsohon Firayim Minista Rishi Sunak ya sanar.

 “Wannan wata shawara ce daga gwamnatin da ta gabata wadda ba a gabatar da ita gabanin zabe ba kuma zan iya tabbatar da cewa gwamnati ba za ta bi ta ba, in ji kakakin Firaministan Birtaniya.

A watan Mayu da ya gabata ne mai gabatar da kara na kotun ICC, Karim Khan, ya zargi Benjamin Netanyahu, da ministan tsaron Isra’ilar, Yoav Gallant da shugabannin Hamas uku – Yahya Sinouar, Mohammed Deif da Ismaïl Haniyeh – da laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a zirin Gaza da kuma Isra’ila.

Netanyahu da sauran shugabannin Isra’ila sun yi Allah wadai da matakin a matsayin abin kunya da kyamar Yahudawa.

Shugaban Amurka Joe Biden ma ya soki mai bukatar ta mai gabatar da kara na kotun tare da goyan bayan hakkin Isra’ila na kare kanta daga Hamas – kamar yadda Mista Sunak ya yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments