Gidan rediyon kasar Habasha “Fana” ya watsa rahoton cewa: Majalisar al’ummar kasar Habasha ta ayyana zaman makoki na tsawon kwanaki uku domin nuna alhini da juyayi ga wadanda bala’in zaftarewar kasa ya rutsa da su a yankin Gezi Gofa da ke kudancin kasar.
Bayanai da suke fitowa daga kasar Habasha suna nuni da cewa: Adadin mutanen da suka mutu sakamakon zaftarewar kasa a Habasha na iya kaiwa mutane 500, a cewar wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar.
Bala’in ya afku ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a ranar Litinin da ta gabata a wani yanki mai tsaunuka a kudancin kasar ta Habasha.
Kudancin Habasha dai na fuskantar karancin ruwan sama tsakanin watannin Afrilu da farkon Mayu, wanda ke karuwa a cikin watannin Yuli da Agusta da ke haifar da ambaliya da zabtarewar laka.