Yunkurin Hukumar Falasdinu Na Kama Kwamandan Gwagwarmaya Taimako Ne Ga ‘Yan Sahayoniyya

Yunkurin hukumar Falasdinawa na neman kama kwamandan ‘yan gwagwarmayar birnin Tul-Karam babbar hidima ce ga yahudawan sahayoniyya Mamba a ofishin siyasa na kungiyar Jihadul- Islami

Yunkurin hukumar Falasdinawa na neman kama kwamandan ‘yan gwagwarmayar birnin Tul-Karam babbar hidima ce ga yahudawan sahayoniyya

Mamba a ofishin siyasa na kungiyar Jihadul- Islami ta Falastinu, kuma babban jami’in kungiyar a kasar Lebanon Ali Abu Shaheen, ya jaddada cewa: Abin da hukumar cin gashin Falasdinawa ta yi na yunkurin kame kwamandan bangaren sojin Sarayal-Qudus na kungiyar jihadul-Islami a birnin Tulkaram, wata babbar hidima ce ga makiya yahudawan sahayoniyya, wadanda ke neman farauta da kawar da ‘yan gwagwarmayar Falasdinu.

Abu Shaheen ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a jiya Juma’a, inda ya ce: Kyakkyawan tarbar da aka yi wa kwamanda Abu Shuja’a (Kwamandan Bataliyar Tulkaram) a sansanin Nour Shams, da kuma tattakin da jama’a suka yi zuwa asibiti domin kawo karshen killace shi da a ka yi lamari ne dake tabbatar da matsayin al’ummar Falasdinu na goyon bayan gwagwarmayar da ake yi a yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye, wanda aniyar hukumar Falasdinawa take nufin cewa tana adawa da al’ummarta.

Abu Shaheen ya jaddada cewa: Kungiyar Jihadul- Islami ba za ta kasance cikin fadace-fadace da ke gudana tsakanin Falasdinawa ba, kuma ba za ta janye daga fada da tunkarar makiya yahudawan sahayoniyya a dukkanin fagagen ba.

Yana mai tabbatar da imanin al’ummar Falastinu cewa: Sun yi Imanin gwagwarmaya da makami ne kawai hanya daya tilo ta tunkarar makiya da kuma fatattakar su daga yankunan Falasdinawa da suka mamaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments