Sakamakon wani kuri’ar jin ra’ayin jama’a a haramtacciyar kasar Isra’ila da aka gudanar a baya-bayan nan ya nuna cewa: ‘Yan adawa da masu goyon bayan fira minista Benjamin Netanyahu ba zasu samu isassun kujeru da za su iya kafa sabuwar gwamnati su kadai ba idan aka gudanar da zabe a haramtacciyar kasar a halin yanzu.
Kuri’ar jin ra’ayin jama’a da Cibiyar Lazar (mai zaman kanta) ta gudanar da jaridar haramtacciyar kasar Isra’ila ta “Ma’ariv” ta watsa tana nuni da cewa: Gungun ‘yan adawa yahudawan sahayoniyya za su sami kujeru 57 a majalisar dokokin haramtacciyar kasar Isra’ila ta Knesset cikin kujeru 120.Yayin da magoya bayan fira minista Netanyahu, zasu samu kujeru 53, sannan jam’iyyun Larabawa za su samu kujeru 10, idan aka gudanar da zabe a haramtacciyar kasar Isra’ila a halin yanzu haka. Don haka dole ne kowane bangare ya neman kulla kawance da wani bangare domin samun wakilai 61 domin samun damar kafa sabuwar gwamnati.